Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Ya kara da cewa Iran ta shiga tattaunawar ce da kyakkyawar Niyya kuma ta yi amfani da hanyoyin da za su karfafa daya bangaren wajen amfani da hikima da zurfin tunani a wajen tattaunawar
Da yake bayani game da makircin da isra’aila take kullawa na ganin tattaunawar bata yi nasara ba y a fadi cewa: “Isra’ila tana kokarin yin zagon kasa daga wajen dakin taron yadda zai yi tasiri a sakamakon tattaunawar da za’a fitar daga karshe,
Ya ce a tattaunawar zagaye na 7 da aka yi Iran ta kaddamar da daftarin kuduri guda 2 , na farko ya mayar da hankali ne game da batun cire mata dukkan takunkuman da aka kakaba mata, na biyu kuma game da aikace-aikacen ta na makamashin nukiliya na zaman lafiya,
Iran ta mayar da hankali kan batun cire mata takunkumi , kuma ta jaddada cewa ba za ta amince da wata sabuwar Yarjejeniya da ta wuce wadda aka cimma a shekara ta 2015 ba.
342/